Kano: An ɗaura auren mutane dubu

A jihar Kano dake arewacin Najeriya ɗazu ne aka ɗaura auren mutane dubu daya karkashin shirin gwamnatin jihar na tallafawa al'umma.

Wannan dai shi ne karo na uku da hukumar ta Hizba take gudanar da irin wannan aure, kuma na wannan karon shi ne mafi yawan ma'auratan, tun bayan da hukumar ta bullo da tsarin aurar da zawarawa a jihar, da nufin rage yawan mace-macen aure.

An dai gudanar da ɗaure-ɗauren auren na yau din ne a dukkan ƙananan hukumomin jihar, yayin da kuma aka ɗaura auren mutane ɗari a babban masallacin juma'a na birnin Kano.

Jihar Kano dai na daga cikin jihohin Najeriya inda ake fama da matsalar yawan mutuwar aure.