An kama mamallakin ginin da ya rufta a Bangladesh

Masu aikin ceto a Bangladesh
Image caption Ana fargabar cewa har yanzu akwai daruruwan mutane a karkashin baraguzan ginin

An kama mutumin da ya mallaki ginin nan dake dauke da masana'antun saka tufafi a Bangladesh, wanda ya ruguje ranar larabar da ta wuce, inda daruruwan mutane suka mutu.

'Yan sanda sun ce Mohammed Sohel Rana, wanda ya shiga buya tun lokacin da lamarin ya faru, an kama shi ne a jahar Belgal ta Yamma dake kusa da kan iyaka da India.

Jama'a dai sun yi ta suwwa lokacin da aka bada sanarwar kama shi.

A halin da ake ciki kuma, sojoji na shirin amfani da manyan injinan daga kaya masu nauyin gaske domin kwashe tarkacen ginin yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da kokarin kaiwa ga wadanda ke raye a ciki.

Kawo yanzu dai an samu ceto akalla mutane dubu 2 da dari 4 daga cikin ginin mai hawa 8 dake wajen birnin Dhaka.

Sama da mutane dari 3 da sittin ne aka tabbatar sun mutu a hadarin.

Karin bayani