Gobara ta tashi a ginin da ya rufta a Bangladesh

Masu aikin ceto a Bangladesh
Image caption Masu aikin ceto a Bangladesh

Wata gobara ta tashi a cikin baraguzan ginin nan da ya ruguje ranar laraba a Bangladesh, abin da ya kawo cikas ga kokarin da ma'aikatan ceto ke yi na fito da mutanen da har yanzu ke da rai makale a ciki.

Tartsatsin wutar da ke tashi ne daga karafan da masu aikin ceto ke yankawa, ta haddasa gobarar, wadda yanzu mahukunta suka ce sun shawo kanta.

An garzaya da ma'aikatan kashe gobara 4 zuwa asibiti.

Wata mata da ma'aikatan ceton suka kwashe sa'o'i suna kokarin janyowa daga karkashin baraguzan ginin, sun ce yanzu ta rasu.

Tun da farko dai an kama Muhammed Sohal Rana, mutumen da ya mallaki ginin da ya rufta, bayan da ya shiga buya tun bayan afkuwar lamarin.

Wakilin BBC ya ce kawo yanzu an kama mutane shida da suka hada da masu masana'antun saka tufafi uku da ke cikin ginin.

Karin bayani