Kura ta lafa a garin Diffa na Jumhuriyar Nijar

Matatar man Nijar dake garin Dan Baki
Image caption A shekara ta 2011 ne, Nijar ta fara hako man fetur a yankin Agadem na jihar Diffa

Rahotanni daga jihar Diffa dake Gabashin Jumhuriyar Nijar, sun ce yanzu kura ta lafa a garin Diffa, bayan wani dauki ba dadi da aka yi a jiya Asabar tsakanin matasa garin da jami'an tsaro, abun da ya yi sanadiyyar jikatta mutane 4.

Al'amarin dai ya faru ne a lokacin da matasan ke gudanar da zanga- zanga saboda matsalar rashin aikin yi da suka ce ta addabe su.

Matasan wadanda suka lalata dukiyoyi masu yawa a lokacin zanga- zangar, na zargin hukumomi ne da mayar da su saniyar ware wajen dauka aiki a cibiyar hakar man fetur ta Agadem da ke yankin.

Yanzu haka dai, Firayim ministan kasar ta Nijar, Malam Brigi Rafini yana garin na Diffa inda yake tattaunawa da shugabannin matasan da na al'umma da kuma hukumomin jihar kan yadda za a shawo kan matsalar.

A shekara ta 2011 ne dai Nijar ta fara aikin hakar man fetur a yankin na Agadem tare da hadin gwiwar wani kamfanin kasar China.

Karin bayani