"Ina fushi da 'yan siyasa" Inji Luigi

Mutumin da ya harbi 'yan sanda biyu ya ji musu ciwo a lokacin da ake bikin rantsar da sabuwar gwamnatin gamin gambizar kasar Italiya ya fadawa masu gudanar da bincike cewa ya yi hakanne kan bakin cikinsa da 'yan siyasa.

Lamarion ya faru ne a wajan ofishin sabon praministan kasar Enrico Letta, dake da nisan kusan kilo mita daya daga fadar shugaban kasar, inda ake bikin rantsar da sabuwar gwamnatin.

Nan take dai aka kama dan bindigar, mai suna Luigi Preiti.

Sabon ministan cikin gidan Italiyan ya kwatwanta lamarin a matsayin wani bakincikin da wanda bai da aiki ke ciki.