Takaddun jirgin Ameachi sun gama aiki! NCAA

Hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama a Nijeriya, NCAA ta dakatar da jirgin saman gwamnan jihar Rivers daga tashi.

Hukumomin kula da harkokin jiragen saman sun ce an dakatar da jirgin ne sabilida takardun lasisinsa sun gama aiki.

Tuni dai ake zargin cewa dakatar da jirgin gwamnan jihar Rivers din ba zai rasa nasaba da takun sakar da ya ke da shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ba.

A wani labarin kuma a jahar ta Rivers rundunar samar da tsaro ta JTF a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur tace ta kama wadanda take zargin masu satar mai ne su 76 ta kuma kama wasu daga cikin jiragen satar man, sannan ta lalata wuraren hakar mai wadanda bana hukuma ba guda 28 a jahar.

Rundunar tsaron dai ta bayyana hakan ne a wata sanarwa data fitar bayan samamen da ta kai a yankin domin dakile matsalar satar mai.