Ana tuhumar mamallakin ginin da ya rufta a Bangladeh

Daya daga cikin wadanda ruftawar ginin ta rutsa da su a Bangladesh
Image caption Daya daga cikin wadanda ruftawar gini ta rutsa da su a Bangladesh

Ana tuhumar mamallakin ginin da laifin yin sakaci ne, tare da wasu injiniyoyin gwamnati biyu da keda hannu wajen amincewa da ginin.

An cafke mutumin Mohammed Sohel Rana, a kusa da kan iyakar yammacin kasar da India, bayan da ya gudu tun lokacin da lamarin ya abku.

Yanzu dai an shiga rana ta shida na aikin ceto cikin baraguzan ginin nan da ya ruguje, amma kuma jami'ai sun bayyana cewa sun yanke kaunar samun wasu dake da rai a ciki.

Tuni dai aka yi watsi da ayyukan ceto mai wahalar gaske da ake yi da hannu inda aka fara amfani da wasu injina don dage baraguzan ginin da suka rufta.

Rahotanni sunce ginin benen ya nuna alamun tsagewa kwana guda kafin ya ruguje, sai dai kuma an yi watsi da batun abinda ka iya biyo baya.

An dai gudanar da zanga-zanga a Dhaka babban birin kasar ta Bangladesh, kan batun yanayin aiki a masana'antun dinka riguna.

Masu zanga-zangar sun yi jerin gwano a gaban ofishin kungiyar ma'aikatan masana'antun dinka riguna na kasar suna rera take da daga kwalaye dauke da rubutu.

Daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar Shariar Sony, ya dora alhakin rashin kai daukin gaggawa kan gwamnatin kasar.