An fara yanke kaunar ceto mutane a Bangladesh

Banglladesh
Image caption Banglladesh

An fara yanke kauna ga yunkurin ceto wasu daruruwan mutane da ke karkashi baraguzan dogon benen nan da ya rushe a Bangladesh.

Ya zuwa yanzu dai an zakulo gawarwakin mutane sama da dari uku da saba'in.

Hukumomin kasar ta Bangladesh sun ki amincewa da tayin da wasu kasashen duniya suka yi na kai masu dauki a ayyukan ceton.

Ma'aikatan ceto na kasar sun shafe kwanaki shidda suna ta wannan aiki, inda suke kokarin daga manyan bangwayen kankare domin kaiwa ga wadanda aka rutsa da su a karkashi.