An amince da dokar rage guraban ayyuka a Girka

Masu zanga-zanga a kasar Girka
Image caption Masu zanga-zanga a kasar Girka

Majalisar dokokin kasar Girka ta amince da kudirin dokar da za ta baiwa gwamnati damar rage guraban ayyuka goma sha biyar a ma'aikatunta.

Wannan garanbawul wani sharadi ne da zai baiwa kasar ta Girka damar samun karin tallafin kasa da kasa na dala biliyan goma sha biyu.

Sabuwar dokar dai zata kawo karshen tabbacin da duk wani ma'aikacin gwamnatin kasar ke da shi, na wanzuwar rayuwar aiki.Hakan dai ya haifar da zanga-zanga a gaban ginin majalisar dokokin.

Masu zanga zangar sun yi hakan ne don fargabar da suke da ita, na yiwuwar karuwar rashin aikin yi a kasar da tuni yayi katutu, a bisa wannan doka.

Wani daga cikin masu zanga-zangar, Basilis Liosis, ya ce dokar zata shafi mutane da yawa, ta fannoni da dama.

Ta wani gefen kuma wani mutum daga cikin masu anga-zangar kokawa yake cewa mutane da dama basu fito sun shigazanga-zangar ba.

Ya ce abin takaici ne mutane ba sa amsa kiran daga kungiyoyi da jam'iyu na a fito zanga-zanga.

Ita dai gwamnatin kasar ta ce, wannan doka za ta kawo sauyi tare da inganta ayyukan ma'aikatun nata, ta hanyar zaftare ma'aikatan da basu da da'a, da kuma samarwa masu jini a jika da kuma hazaka guraban ayyuka.