Takaddamar Ameachi da Jonathan na shafar PDP

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Sa-in-sar da ake yi tsakanin Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya da Shugaban Kungiyar gwamnonin kasar, Gwamna Rotimi Amaechi na jihar Rivers na ci gaba da dagula rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar ta PDP.

Takaddamar dai ta samo asali ne a cewar wasu saboda irin adawar da Gwamna Ameachi ya ke yi da daga aniyar da Shugaban ke da ita ta neman wa'adi na biyu na mulki.

Rahotanni daga Nijeriyar sun nuna cewar wasu kusoshin jam'iyyar suna nuna fargaba cewar wannan rikici zai iya nakasa jam'iyyar a yayinda babban zaben kasar ke karatowa a shekara ta 2015.

Koda a cikin makon da ya wuce dai takaddamar ta kai ga hana wa Gwamnan tashi da jirginsa.