Burtaniya zata dakatar da baiwa Afrika ta Kudu tallafi

Kasar Afirka ta Kudu
Image caption Kasar Afirka ta Kudu

Burtaniya ta fara yunkurin dakatar da baiwa kasar Afrika ta Kudu tallafin da ta saba bayarwa daga shekara ta 2015.

A yau talata ne Sakatariyar dake kula da hukumar raya kasashe masu tasowa Justine Greening, zata sanar da kawo karshen shirin bada tallafin da ya kai kimanin dala miliyan talatin a kowace shekara.

Jami'ai sun ce an yanke shawarar yin haka ne saboda irin nasarorin da kasar ta Afrika ta kudu ta samu, tun bayan da aka kawo karshen mulkin wariyar launin fata, inda ake ci gaba da kallon kasar a matsayin wacce ita kanta ta cancanci ta rika bada tallafi.

Kasar Afrika ta kudu dai ita ce ke samar da sama da kashi daya bisa uku na arzikin cikin gida na kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, kuma daya daga cikin kungiyar kasashen dake samun bunkasar tattalin arziki ta BRICS .