Likitoci sun fara duba fursunoni a Guantanamo

Gidan kurkukun sojin Amurka na Guantanamo
Image caption Gidan kurkukun sojin Amurka na Guantanamo

Wasu karin likitoci da ma'aikatan jinya kimanin arba'in, sun fara gudanar da aikin yiwa fursunoni magani a kurkukun sojin Amurka na Guantanamo dake Cuba.

Fursunonin sun galabaita ne sakamakon yajin cin abincin da suka fara tun a watan Fabrairu.

Sun dauki wannan mataki ne domin nuna rashin jin dadin su kan yadda tsarewa tare da gallaza musu ba tare da yi musu shari'a ba

Mai magana da yawun rundunar sojin Amurkar Laftanal Samuel House, ya ce fursononi kimanin dari daga cikin dari da sittin da shidan da ake tsare da su ne suka kauracewa cin abincin.

Kimanin ashirin da daya daga cikinsu ake durawa abinci mai ruwa-ruwa ta hanci.

Sai dai wannan mataki na tilastawa fursunonin cin abinci ya kara haifar da rudani game da yadda ake rike da su a sansanin na Guantanamo.

Kungiyar Likitoci ta Amurka ta aikewa da Sakataren harkokin tsaron kasar wata wasika mai dauke da tuhuma game da halin da fursunonin ke ciki.

A shekaru hudun da suka gabata ne dai shugaban Amurka Barack Obama ayi alkawarin rufe sansanin na Guantanamo lokacin da yake gudanar da yakin neman zabe.