An yiwa ma'aikatar shari'a kawanya a Tripoli

Libya

Wasu gungun mutane dauke da muggan makamai sun kewaye ma'aikatar shari'a ta Libya a birnin Tripoli, babban birnin kasar.

Suna nema ne a amince da wata doka mai janyo kace-nace, wadda zata sa a mayar da wasu saniyar ware a harkokin siyasar kasar.

An kirkiro dokar ne da nufin hana tsoffin jami'ai a zamanin tsohon shugaban kasa Kanar Mu'ammar Gaddafi shiga cikin gwamnati.

Ita ma ma'aikatar harkokin wajen kasar na fuskantar irin wannan kawanya tun daga ranar Lahadi.