Netherlands: Willem Alexander ya gaji mahaifiyarsa

Sarauniya Beatrix a takiya, tare da danta Williem da matarsa
Image caption Sarauniya Beatrix a takiya, tare da danta Williem da matarsa

Sarki Willem-Alexander ya gaji mahaifiyarsa Sarauniya Beatrix a matsayin sabon sarkin Netherlands.

Dubban mutane ne suka hallaru a birnin Amsterdam don halartar bikin mika ragamar mulkin sarauniya Beatrix zuwa ga babban danta.

Sarauniya Beatrix ta gudanar da aikinta na karshe, inda ta sanya hannu kan wata takardar nada babban danta Yarima Willem-Alexander a matsayin sabon sarki.

Wannan shine karon farko da hakan ke faruwa a kasar cikin fiye da shekaru dari.

An dai kawata birnin Amsterdam da launin ruwan goro mulukiyar kasar.

Prime Ministan kasar Mark Rutte ya ce, bikin na da matukar muhimmanci, domin ci gaba da tafiyar masarauta ce da kuma kasa.

Mr Rutte ya kuma ce, ya yi amannar sabon sarki Willem-Alexander, zai kasance adalin sarki, zai bi sahun mahaifiyarsa, kakanninsa, dama sauran sarakuna da suka shude wajen gudanar da aikinsa.

A jawabinta na karshe ga al'ummar kasar, sarauniyar ta jadadda cewa wanda zai gaje ta a shirye yake don daukar nauyin tafiyar da mulkin kasar.