Mutane sha hudu sun mutu a Damascus

Syria
Image caption Syria

Syria ta ce mutane akalla sha hudu ne suka mutu sannan wasu fiye da dari daya suka samu raunuka, a lokacin da wani bam ya tarwatse a tsakiyar Damascus babban birnin kasar.

Wannan ne dai hari na biyu a cikin kwanaki biyu, bayan wani harin bam din da ya ci tura, wanda aka kai da niyyar kashe praministan kasar, lokacin da yake wucewa cikin mota da 'yan rakiyarsa.

A waje daya shugaba Obama ya ce Amurka ba ta da masaniya kan yadda aka yi amfani da makamai masu guba Syria, da lokacin da aka yi da kuma ko wane ne yayi amfanin da su.

A wani taron manema labaru a Washington ya ce Amurka na da shaidun cewa an yi amfani da makamai masu guba.

Amma ya ce sai sun tabbatar da sahihancin hujjojinsu kafin su san matakin da zasu dauka.

Karin bayani