Afrika ta Kudu ta soki Birtaniya kan tsayar da agaji

Pretoria, Afrika ta Kudu
Image caption Pretoria, Afrika ta Kudu

Kasar Afirka ta kudu ta soki lamirin Birtaniya game da dakatar da baiwa kasar gudunmawar agaji kai tsaye.

Gudunmawar dai ta kai ta tsabar kudi dala miliyan talatin a shekara.

A cikin wata sanarwa, gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce shawarar da Birtaniyar ta yanke a jiya, ta yi shi ne gaba-gadi, tana mai cewa zai yi mumman illa ga ayyukan da gwamnatin ke gudanarwa a halin yanzu.

Sashen bada taimakon raya kasashe na Birtaniyar ya ce an dauki hukuncin ne bayan tattaunawa da kasar Afrika ta kudun, da kuma nazarin cigaban da aka samu bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata.

Sai dai kuma wani dan majalisar Birtaniyar na bangaren adawa Ivan Lewis ya ce matakin zai shafi dangantakar Birtaniya da Afirka ta kudu.

Ya ce, "ko kadan ba haka ba ne, wannan babu shakka zai bata dangantakarmu da muhimmiyar kasar da muke abokantaka da ita."