Yansanda sun yi sabon kame a Boston

Harin bam a Boston
Image caption Harin bam a Boston

'Yan sanda a birnin Boston na Amirka sun ce sun kama karin wasu mutane uku wadanda ake zargin suna da hannu a harin bam din da aka kai lokacin tseren yada kanin wani na Marathon a watan da ya gabata.

An dai kashe mutane uku da jikata wasu mutanen fiye da dari biyu da sittin a harin.

Ana tsammanin cewa biyu daga cikin mutanen da aka kama yau abokan karatu ne a jami'a ga Dzhokhar Tsarnaev a mutumin da ake tuhuma da kai harin.

Karin bayani