An zargi hukumomin Nigeria da yin rufa-rufa a Baga

Garin Baga
Image caption Garin Baga

Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Rights Watch ta yi kira ga hukumomin Nigeria da su gudanar da bincike tsakani da Allah su kuma hukunta duk wasu sojoji da aka samu da alhakin hallaka farar hulla da kona gidajen mutane a rikicin baya bayan nan a garin Baga na Jihar Borno a Nigeria.

Kungiyar kare hakkin bil-adamar ta yi amfani da hotuna na tauraron dan adam domin gano girman barnar da aka yi a garin na Baga da ke kusa da tafkin Chadi.

Gwamnatin Nigeria ta ce farar hulla 6 ne suka mutu da kuma wadanda ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram 30 a fadan da aka yi tsakanin sojoji da 'yan kungiyar.

Saidai kuma wasu jama'a sun bayyana cewar mutane fiye da 200 ne suka mutu a rikicin.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce daga nazarin da ta yi akan hotunan tauraron dan, akwai banbanci matuka tsakanin abun da ya wakana da kuma sanarwar da hukumomin Nigeria suka fitar.

Kungiyar ta ce hukumomi na kokarin rufa-rufa akan ta'asar da ta ke zargin sojoji sun tafka.

Tauraron dan adam

Kungiyar Human Rigths Watch ta ce ta gudanar da bincike kan hotunan na garin Baga da ta dauka ta hanyar tauraron dan adam, wanda kuma suka nuna cewa da akwai banbanci matuka tsakanin hakikanin gaskiyar abun da hotunan suka nuna da kuma abun da hukumomin Najeriya suka dage a kai na cewa ba a yi barna sosai ba a harin da aka kai a garin.

A hotunan da ta wallafa, kungiyar ta Human Rights Watch ta nuna yadda a bangaren da aka yi ta'adi mai yawa kadai, akwai gidajen zama da na gudanar da harkokin kasuwanci kusan 2,400 da aka lalata ko kuma aka yiwa mummunar illa.

Dukkanin wadannan wurare kuma a yankin kudu ne na garin na Baga.

Kungiyar ta kuma ce dukkanin wadannan gine gine da abun ya shafa, sun nuna alamun gobara ce ta shafe su.

Human Rights Watch ta nuna cewa da alama hukumomi na kokarin yin wata rufa-rufa ne kan hakikanin gaskiyar lamarin.

Kungiyar dai ta nuna hotunan tauraron dan-adam na garin na Baga gabanin afkuwar rikicin, sannan kuma ta nuna hotunan bayan wannan rikici.

Ga kuma duk wanda ya kalli hotunan zai shaida lalle akwai mummunan ta'adi da aka yiwa wani sashe na garin.

Tawagar gwamnati

Kungiyar kare hakkin bil-adaman ta yi kira ga hukumomin Nigeria da su gudanar da bincike tsakani da Allah su kuma hukunta duk wasu sojoji da aka samu da alhakin hallaka farar hulla da kona gidajen mutane a rikicin baya bayan nan a garin Baga na Jihar Bornon Nigeriar.

Gwamnatin Nigeria ta ce farar hulla 6 ne suka mutu da kuma wadanda ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram 30 a fadan da aka yi tsakanin sojoji da 'yan kungiyar.

A ranar Talata ne, wata tawagar sojoji da ta ce ta ziyarci garin na Baga domin tantance abun da ya wakana, ta mika rahotonta na wucin gadi ga gwamnati tare da hukumar aikace-aikacen gaggawa ta kasa wato NEMA.

Tawagar sojojin ta nace akan cewar, ta yiwa mutane da dama tambayoyi a garin na Baga, domin su nuna mata manya-manyan kaburbura da ake zargin an binne wadanda suka mutu, ba tare da sun nuna mata ba.

Haka nan kuma tawagar ta musanta batun cewar an kona gidaje fiye da dubu 3.

'Yan siyasa daga jam'iyun bangaren adawa na cigaba da nuna adawa ta kin amincewa da kalaman bangaren gwamnatin tare da cewa akwai matsala da sarkakiya cikin lamarin.