An daure wani ba Amurke a Koriya ta arewa

Image caption Kenneth bea tare da abokinsa

Kafar yada labaran Koriya ta arewa ta ce an yanke wa wani dan kasar Amurka hukuncin zama a gidan kaso har na tsawon shekaru goma sha biyar tare da aiki mai wahala.

Pae Jun Ho wanda ake kiransa da suna Kenneth Bae a Amurka, ya shiga koriya ta arewa tun a watan nuwamba a matsayin dan yawon bude ido.

Rahotanni daga kafafan yada labaran Koriya ta arewa sun ce, ana zargin mutum ne da kokarin hambarar da gwamnatin kasar.

Wannan lamari dai ya zo adai-dai lokacin da ake zaman dar-dar tsakanin Washington da Pyonyang, tun bayan da Koriya ta Arewa ta gwada makamanta masu linzami a watan fabrairu.