A yau ne ake bikin ranar ma'aikata ta duniya.

Ma'aikata
Image caption Ma'aikata

A yau ne ake bukukuwan tunawa da zagayowar ranar ma'aikata a fadin kasashen duniya.

Majalisar dinkin duniya ta ware duk ranar daya ga watan Mayu na kowace shekara ne, don nuna irin gudunmuwar da ma'aikata ke bayarwa a harkokin yau da kullum, da kuma fito da matsalolin da ma'aikatan ke fuskanta don magance su.

Kasashe sama da Tamanin a fadin duniya ne dai ke yin hutu a wannan ranar, yayinda a wasu kasashen, ma'aikata kan gudanar da fareti, tare da shirya tarurruka dabam dabam.

Sai dai da dama daga ma'aikata a kasashe masu tasowa har da Najeriya na cewa ranar ba ta da wani amfani a wajen su, tun da bukukuwan ranar ba yasa su samu wani sauyi a rayuwar su ta aiki.

Ma'aikata a irin wadannan kasashe sun jima suna kokawa da irin halin kuncin da suka shiga na rashin kulawa da kyautata jin dadin su daga hukumomin.