Facebook ya bayar da kai bori ya hau

Facebook
Image caption A 'yan kwanakin nan ne Facebook ya bayyana samun karin riba a harkokinsa

Shafin sada zumunta na Facebook ya amince ya cire wasu hotunan bidiyo masu tayar da hankali daga shafin na sa.

Wasu daga cikin hotunan sun bayyana a shafin ne tun a makon da ya gabata.

Tun da farko Facebook ya ki bayar da kai bori ya hau game da matsin lambar ya cire hotunan yana mai cewa jama'a na da ikon bayyana ra'yoyinsu kan al'amuran duniya.

Jama'a da dama ne suka rinka yin Allah wadai da wallafa hotunan bidiyon sannan aka rinka musayar bayanai a kansu.

Karin bayani