An ɗaure McCormick shekaru 10

Image caption James McCormick, zai yi shekaru goma a gidan kaso

An yankewa ɗan Birtaniya, James McCormick ɗaurin shekaru goma saboda zamba wajen saida na'urorin jabu ga ƙasashen da suka haɗa da Iraqi, da kuma Nijar.

ayin yankewa mutumin hukunci daurin shekaru goma, alkalin kotun Old Bailey dake nan London yace, McCormick ya aikata gagarumar zamba dake cike da cin amana. Alkalin kotun ya kuma bayyana irin ribar da McCormick ya samu a matsayin mummuna, da kuma ta haddasa mutuwa da cutar da wasu mutane.

Alkalin kotun Richard Hine ya kuma ce, dan kasuwar McCormick mazambaci ne da ya rika yaudarar abokan huldarsa.

Ana dai zaton James McCormick ya samu ribas kusan dalar Amurka miliyan tamanin wajen cikin naurar da ta bogi ce, da yace, za'a iya amfani da ita wajen gano muggan kwayoyi da kuma bama-bamai. Sai dai kuma tun farko lauyansa yace, anyi amfani da wasu daga cikin na'urorin da wanda yake karewa ya sayar sun yi aiki, kuma yace, babu wata hujjar cewa, wasu na'urorin da ya sayar sun haddasa asarar rayuka.

Gwamnatin Nijar dai kashe kimanin dalar Amurka dubu dari biyu wajen sayen na'urorin da mutumin yake sayarwa a shekara ta 2008 bayan mutumin da kotu ta kira mazambaci ya yi gwajin na'urorin na bogi.