Turai ta yi nasara kan Patience Jonathan

Patience Jonathan
Image caption Patience Jonathan ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin

Wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukuncin cewa an yi kuskure wurin kwace wani fili daga hannun cibiyar Hajiya Turai Yar'adua domin baiwa African First Lady Peace Mission ta uwar gidan shugaba Goodluck Jonathan.

Mai shari'a Peter Affen ya ce ma'aikatar birnin Tarayya Abuja ta yi kuskuren soke lasisin fulotin mallakar Women Youth Empowerment Foundation.

Sannan ya bayar da umarnin a mayarwa da gidauniyar ta Turai Yar'adua fulotin na ta.

Sai dai Bangaren Patience Jonathan sun ce za su daukaka kara.

'Ko wanne ya ja tunga'

Kotun ta ce anyi kuskuren karbe fulotin daga karkashin ikon Women and Youth Empowerment Foundation na Turai Yar'adua inda aka baiwa Uwar gidan Shugaba Goodluck Jonathan, don gudanar da aiyukan ofishin African First Lady Peace Mission.

A watan Nuwamban bara ne Ministan Birnin Tarayya Abuja Sanata Bala Mohammed ya soke lasisin mallakar fulotin na Gidauniyar tallafawa mata da matasa na Hajiya Turai Yar'adua.

Ministan ya baiwa Uwar gidan Shugaban kasa Patience Jonathan filin ne domin gudanar da aiyukan ofishin Kungiyar samar da zaman lafiya ta matan shugabannin Afrika wato African First Lady Peace Mission Project wanda take jagoranta.

Kotun kafin wannan ranar, ta baiwa bangarorin biyu damar yin sulhu a wajen kotu amma ko wanne ya ja tunga kan ikirarin cewa shi ne da mallakar fulotin.

Karin bayani