Huldar kasuwanci tsakanin Najeriya da Canada

Mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo
Image caption Harkokin kasuwanci na kara bunkasa tsakanin kasashen biyu

Manyan jami'an Najeriya karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo, sun gudanar da taron yini biyu domin karfafa hulda da zuba jari tsakanin Najeriya da kasar Canada.

Taron ya duba yadda kasashen biyu za su amfana ta hanyar cinikayya da zuba jari a tsakaninsu.

Fira ministan Canada Stephen Harper da mataimakin shugaban Najeriya Namadi Sambo, sun gana gabanin taron inda suka amince a kafa wata hukuma da za ta bunkasa zuba jari tsakanin kasashen biyu.

Sai dai taron ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da matsalar tsaro a wasu sassan kasar, abinda wasu masu sharhi a kan al'amura ke cewa zai iya kawo tarnaki ga zuba jari a kasar.

Amma wasu masu zuba jari na kasar ta Canada, sun ce wannan ba zai hana su zuba jari a Najeriyar ba, domin bangaren da za su zuba jarin zai ma taimaka ne wajen magance matsalar tsaron.

Wasu daga cikin masu zuba jarin na kasar Canada sun ce za su mayar da hankali ne a bangaren makarantun kimiyyar kere-kere don samar da ma'aikata masu inganci da ake bukata, sabanin wadanda makarantun kasar ke samar wa a yanzu wadanda suka san abubuwa a rubuce ba a aikace ba.

Tsarin karatun Najeriya na yanzu

Mr Paul Brennan, babban jami'i ne a kungiyar makarantun kimiyya na Canada, ya kuma ce, daya daga cikin matsalolin da ke haifar da rashin tsaro a kasar shi ne rashin aikin yi ga dimbin matasa a kasar, wanda za a iya magance hakan ta hanyar horar da su sana'oi tun suna makaranta sabanin abinda ake da shi a yanzu:

"Najeriya ce babbar kawar Canada a harkar kasuwanci a nahiyar Afrika, sai dai idan muna son zuba jarinmu ya yi nasara, to za mu bukaci kwararrun ma'aikata 'yan asalin Najeriya da suke da kwarewar da ake bukata don yin aikin.

Kuma a tsarin karatun Najeriya na yanzu, yawancin daliban da ake horar wa ba su da kwarewar da ke da alaka da irin ayyukan da ake samarwa a harkokin zuba jari," a cewar Mr Paul.

Ya kara da cewa a don haka akwai bukatar a kawo garambawul a tsarin ilimin koyar da sana'oi a Najeriya, maimakon mayar da hankali kan ilmin jami'a kawai.

Ya kuma ce yin hakan zai taimaka wajen rage matsalolin rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya, ta hanyar samarwa da dimbin matasa da ke kammala karatu a kowacce shekara hanyoyin dogaro da kai maimakon jiran samun aikin gwamnati ko bangarori masu zaman kansu.

A baya-bayan nan dai kasashen biyu sun yunkuro wajen bukasa cinikayya da ke tsakaninsu inda kididdiga ta nuna cewa an samu bunkasar ciniki tsakaninsu da a yanzu ya haura dala miliyan dubu biyu.

Karin bayani