An kashe mutane da dama a Syria

Tashin hankali a Syria
Image caption Tashin hankali a Syria

Mutane akalla 40 ne aka kashe a kauyen Beida dake kudancin birnin Tartous mai tashar jiragen ruwa na Syria.

Wata kungiyar masu fafutika da ake kira Cibiyar tattara keta hakkoki a Syriar ta zayyana sunayen mutane 42 da ta ce an yi masu kisan gilla ne, kuma sun hada da yara 3 da mata 6.

Kungiyar sa ido kan kare hakkin Biladama a Syria da take da zamanta a nan London ta ce wasu daga cikin wadanda suka mutu din a Al-Beida an kashe su ne da wukake, wasu kuma an harbe su ne a kurkusa.

Kafofin watsa labarai na gwamnatin Syria sun bayar da rahoton cewar dakarun gwamnati sun kasance a yankin, kuma sun kashe abinda suka bayyana a matsayin 'yan ta'adda.

Zargin kisan kiyashin da ake yiwa dakarun gwamnati da kuma sojin sa kai na Alawi da ake kira Shabbiha sun yi wa wasu mutanen kauyukan 'yan sunni, ba zai yi wani abu don rage karuwar korafe-korafen nunin banbancin addini ba.

Yayin da 'yan Alawi tsiraru da suka kankane gwamnati ke gwagwarmayar dorewa a kan wani boren da ya taso daga al'ummar 'yan sunni masu rinjaye.

Karin bayani