Amurka da Mexico za su karfafa dangantaka

Shugaba Obama tare da takwaransa na Mexico, Enrique Pena Nieto sun yi alkawarin mai da hankali wajen karfafa danganta akan kasuwanci da kuma samar da ayyukan yi.

Da ya ke jawabi a lokacin ziyarar sa ta farko kasar Mexico tun bayan sake zabar sa, Shugaba Obama ya ce, yawan bakin haure da ke shiga Amurka ba bisa ka'ida ba ya ragu matuka, hakan kuma na da nasaba da karfin tattalin arzikin da Mexico ke da shi.

Mr. Pena Nieto ya ce zai mayar da hankali wajen tsaurara matakan tsaro musamman saboda tashe-tashen hankulan da kasar ke fuskanta wajen yaki da miyagun kwayoyi.

Shugaba Obama ya bayyana cewa, Amurka zata cigaba da hada kai da gwamnatin Mexico wajen tabbatar da tsaro.

Ya ce; "babban abinda zan ce ga shugaban , shi ne muna goyon bayan gwamnatin Mexico kan aniyar ta na mai da hankali wajen rage tashe-tashen hankula, zamu ci gaba da hada kai ta kowacce hanya dan ganin an cimma nasara akan wannan kuduri.