Malaysia: Yan adawan sun zargi Fira Minista

Fira Ministan Malaysia Najib Razak ya musanta zargin da ake mishi cewa yana da hannu wajen diban dubun dubatar masu kada kuri'a ta jiragen sama a dai-dai lokacin da kasar ta dauki haramar fara zaben kasa a gobe Lahadi.

'Yan adawa sun zargin Fira ministan ta shatar jirgi domin kai masu kada kuri'a inda yake ganin ba zai yi tasiri.

'Yan adawan kasar dai sunyi zargin ne bayan an kwarmato wasu takardun sakon email da kuma sunayen fasijojin jiragen da suka yi zargin ayi shata.

Bayanan dai sun yi nuni da cewa gwamnati na safarar masu goyon bayanta zuwa gundomomin da suke ganin baza su yi tasiri ba.

Sakonin email din dai sun nuna cewa ofishin Fira Ministan ne ya dauki shatar jirgagen da ke daukar masu Zabe.

Sai dai mai magana da yawun jam'iyya mai mulki ya musanta cewa fira ministan kasar na da hannu a wannan batu.

Sanarwa da jam'iyyar ta fitar ta ce ana taimaka masu kada kuri'a ne kawai domin komawa yankunansu domin su yi zabe.

Wannan dai shine zargi na baya-baya nan da ake yi na cewa gwamnatin kasar na shirya magudin.

Hukumar zaben kasar dai ta ce ta gudanar da shirye-shire tsaf domin ganin a gudanar da zabe karbabbe.