Ana neman kudin fansa kan Ali Munguno

Wata majiya mai karfi ta kusa da daya daga cikin dattawan Jihar Borno da ke arewacin Najeriya wanda wasu 'yan bindiga suka yi awon gaba da shi ta yi karin bayani dangane da maganar da suka yi ta waya da wadanda suka tafi da tsohon ministan.

Jiya ne dai bayan sallar Juma'a aka yi awon gaba da Shettima Ali Monguno; daga bisani kuma 'yan bindigar suka tuntubi iyalan dattijon mai shekaru 87 a duniya suka sada su da shi ta waya.

Majiyar ta kuma bayyana bukatun da 'yan bindigar, wadanda ake zargin 'yan kungiyra Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad ne, suka ce sai an biya musu kafin su saki dattijon.

Majiyar wadda ba ta so a ambaci sunanta ko a nadi muryarta ba ta shaidawa BBC cewa yanzu haka iyalan Shettima Ali Monguno suna jira ne su sake ji daga 'yan bindigar da suka yi garkuwa da mahaifin nasu, bayan maganar da suka yi ta waya jiya da yamma.