Sama da mutane dari shida ne suka mutu a Bangladesh

Dubban masu kishin Islama ne suke gudanar da wani babban gangami a Dhaka, babban birnin Bangladesh, suna kiran gwamnati da ta maida hankali wajen aiwatar da dokokin Islama

Ana kuma ci gaba da dauki-ba-dadi tsakanin 'yan sanda da kuma masu fafutuka dake goyon bayan jam'iyyar Hefazat-e-Islam.

Su dai 'yan wannan jam'iyya suna so ne a amince da hukuncin kisa akan duk wanda yayi batanci ga addinin Islama, kuma suna so ne a aiwatar da tsarin ilimi irin na addinin musulunci sau-da-kafa a kasar.

A wani labarin kuma jami'ai a Bangladesh din sun ce, yanzu sun tabbatar mutane fiye da dari shida ne suka mutu yayin da masana'antar saka tufafi ta rushe a birnin Dhaka kwanaki goma sha daya da suka gabata.

Koda yau lahadi an kuma zakulo karin wasu gawarwaki da dama daga baraguzan ginin mai hawa takwas.