Adamawa: 'Yan bindiga sun kashe mutane 10

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa a arewacin Najeriya ta tabbatar da kisan da wasu 'yan bindiga suka yiwa mutane goma, kana suka jikkata mutane tara a ƙaramar hukumar Maiha.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawan ya fadawa BBC cewa, wasu 'yan bindiga ne suka aukawa kasuwa da kuma wani coci a kauyen Njilang.

Harin na yau ya kuma jikkata mutane tara a kauyen.

Har yanzu dai ba a kama kowa ba dangane da wannan hari.

Jihar Adamawa dai ta sha fama da hare-hare cikin 'yan watannin nan.