Somalia: Bam ya hallaka mutane 8

Image caption Birnin Mogadishu ya sha fama da hari ƙunar baƙin wake

A Mogadishu, babban birnin Somalia, wani harin bam na ƙunar baƙin wake da aka kai da mota ya hallaka mutane takwas kuma wasu da dama suka jikkata.

Rahotanni dai na cewa, harin ya nufi wata motar gwamnati ce dake dauke da wata tawaga ta jami'ai daga Qatar.

Sai dai kuma harin bai samu wadanda aka nufa ba, amma wakilin BBC yace, bam din ya kuma lalata wani gini.

A wani wurin kuma a birnin na Mogadishu sojan gwamnati biya sun jikkata yayin da wani bam da aka binne ya bakin titi ya tashi.

Shugaban Somalia, Hassan Sheik Mahmoud dai yana halartar wani taro a kusa da inda lamarin ya auku, kuma yace, hare-haren suna da nasaba da barazanar da kungiyar Al Shabaab tayi kwanan nan.