Syria ta ce Isra'ila ta kai mata hari

Gida talbijin na gwamnatin Syria ya ce Isra'ila ta kai harin rokoki a kan wata cibiyar bincike da ke wajen garin Damascus.

An dai jikarar tashi bama-bamai kusa da cibiyar Jamraya, inda kasashen yamma ke zargin cewa ana sarrafa makamai masu guba.

Tashin bama-bamai ya girgiza Damascus cikin dare, kuma wasu hotunan bidiyo da aka sanya a shafin Internet sun na cibiyar bincike ta Jamraya na ci da wuta.

Wasu mazauna birnin na Damascus sun shaidawa BBC cewa an kai hari wasu barikin sojoji da ke birnin.

Tun farko dai wasu jam'iyyu Isra'ila da suka ki a bayyana sunayensu sun ce jiragen saman Isra'ila sun kaddamarda hari akan wani taragon makamai masu linzami a cikin Syria a ranar Juma'a.

Jam'ian sun suna kyautata zaton cewa za'a a kaiwa mayakan kungiyar Hezbollah a Lebanon makaman wadda makwabtaka da Syri'an.

Wadannan hare-haren dai sun zo ne bayan masu fafutuka a Syrian sun bayyana cewa dakarun gwamnati sun kashe mutane da dama a wani abu da suka kwatanta a matsayin kisan kiyashi a kusa da garin Albanias, yankin dake gabar ruwa a arewa maso yammacin kasar.

Masu fafutuka sun ce suna da bayanan dake cewa an kashe akalla mutane 77 a unguwannin 'yan shi'a a garin Banias a ranakun Juma'a da Asabar