An kashe mutane 8 a yankin Niger-Delta

Masu fafutika a yankin Niger Delta Najeriya
Image caption Masu fafutika a yankin Niger Delta Najeriya

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa mai aikin samar da zaman lafiya a yankin Niger Delta a Najeriya ta ce ta tsananta tsaro a yankin, bayan da rikici tsakanin 'yan bindiga ya yi sanadiyyar mutuwar mutane takwas.

Kakakin rundunar hadin gwiwa Laftanar kanal Onyeama Nwachukwu, ya ce kisan ya auku ne sakamakon bata-kashi tsakanin bangarorin biyu a ranar Lahadi a garin Yenagoa, babban birnin jihar ta Bayelsa.

Mutanen takwas da aka kashe dukkansu matasa ne, biyar daga cikinsu suna bangaren tsohon jagoran 'yan gwagwarmayar ne Reuben Wilson wanda ya ajiye makamai ya rungumi afuwar da gwamnati ta yi musu a shekara ta 2009.

Jami'an tsaro sun ce a yanzu haka sun killace yankin da aka yi musayar wutar watau Lorbia 1 dake jihar ta Bayelsa inda take gudanar da bincike.

Mai magana da yawun rundunar Onyema Nwachukwu ya shaida wa BBC cewa ba zai iya tabbatar da ko mutane nawa aka kashe ba a yanzu amma dai sun gano gawarwakin biyu daga cikinsu.

Ana fargaba

Laftanar Kanar Onyeman yace sun gano bindigogi biyu kirar Ak47, da kuma wasu bindogin kirar AK47 mai barin wuta guda shidda tare da alburusai.

Har ya zuwa yanzu dai babu wasu bayanai na dalilan da suka haddasa wannan arangama da aka yi.

To amma wannan ba shi ne karon farko ba da kungiyoyin 'yan gwagwarmayar da ke gaba da juna suke kafsa fada wanda kan kai ga hasarar rayuka da hasarar dukiyoyi.

Yawancin fadan ana zargin a kan kudin da ake samu ne ko matsayi ko kuma ramuwar gayya ta wani jinin da aka zubar a baya.

Afuwar da gwamnati ta yi ma 'yan gwagwarmayar a shekara ta 2009 ta saukaka tashin hankalin da ake yi a yankin wanda ya nemi dukusar da aikin hakar man fetur a yankin na Niger Delta.

Sai dai kuma yanzu haka wannan arangamar da ake yi da barazanar da gungun wasu 'yan gwagwarmaya ke yi ta sake daukar makamai sun fara sa fargaba, ga irin tasirin da hakan zai iya haifarwa ga aikin hakar man a yankin na Niger Delta.