An sako Dr Shettima Ali Monguno

Ali Monguno
Bayanan hoto,

A ranar Juma'a ne 'yan bindiga suka sace Dr Ali Monguno

An sako daya daga cikin dattawan jihar Borno da kuma arewacin Nigeria Dr Shettima Ali Monguno, bayan da 'yan bindiga suka sace shi a ranar Juma'a.

Mutanen da suka sace shi ne suka sako shi a ranar Litinin da rana.

"Ina tabbatar da cewa an sako Ali Shettima Monguno," kamar yadda kwamishinan 'yan sandan jihar Borno Abdullahi Yuguda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Jama'a da dama ne suka rinka tururuwa zuwa gidan Dr Monguno domin yi masa marhabin.

Bayan kama dattijon, 'yan bindigar dai sun nemi a biya su kudin fansa.

Kuma wata majiyar tsaro da ta nemi a boye sunanta ta kuma shaida wa AFP cewa, an biya mutanen da suka sace dattijon naira miliyan 50.

Sai dai kwamishinan 'yan sandan ya ki cewa komai game da dalilan da suka kai ga sakin dattijon.

Shi ma mataimakin gwamnan jihar kan harkokin watsa labarai, Isa Umar Gusau, ya shaida wa BBC cewa ba a biya ko kwabo ba domin sako dr Monguno.

Tun da farko gwamnan jihar Borno Kassim Shettima, ya yi kira da wadanda suka sace shi, su yi wa Allah su sake shi saboda tsufansa da kuma taimakon jama'a da yake yi.

Tashe-tashen hankula

Dokta Shettima Ali Monguno ya yi minista a jamhuriya ta farko, kuma yana cikin dattijan arewa.

Dr Monguno yana cikin dattawan da suka gana da shugaban Nigeria Goodluck Jonathan kan yadda za a shawo kan rikicin Boko Haram a Maiduguri a watan Maris.

Ya dade yana kiran da a tattauna da 'ya'yan kungiyar sannan ya nemi shugaba Jonathan ya rage yawan dakarun sojin da aka tura yankin.

Tashe-tashen hankula masu alaka da Boko Haram sun haifar da asarar dubban rayuka tun daga shekara ta 2009.