Najeriya: An kashe mutane 8 a Niger-Delta

Masu fafutika a yankin Niger Delta Najeriya
Image caption Masu fafutika a yankin Niger Delta Najeriya

An kashe a kalla mutane takwas da ke wasu kungiyoyin tsofaffin masu fafutuka biyu da basa ga maciji da juna a yankin Niger-Delta na Najeriya.

Wani kakakin rundunar hadin guiwar samar da tsaro a yankin, Laftanar kanal Onyeama Nwachukwu, ya tabbatar aukuwar lamarin.

Ya ce kisan ya auku ne sakamakon bata-kashi tsakanin bangarorin biyu a ranar lahadi a garin Yenagoa, babban birnin jihar ta Bayelsa.

Kawo yanzu dai ba'a san musabbabin rikicin da ya barke tsakanin tsofaffin masu fafutuka a yankin ba.

Sai dai a baya an sha samun rikice-rikice wajen rabon kudade, ko kuma neman matsayi tsakanin kungiyoyin tsofaffin masu fafutukar da basa ga maci ji da juna.