An kai hare-hare a garuruwan Bama da Banki

Tun shekarar 2009 ne jihar Borno ke fama da tashin hankali
Image caption Tun shekarar 2009 ne, jihar Borno ke fama da tashin hankalin da ya ki ci yaki cinye wa

A Najeriya, wasu da ba a san ko su wanene ba, sun kai hare-hare a kan caji ofis din 'yan sanda a garuruwan Bama da kuma Banki dake jihar Borno.

Har ila yau a garin Bama, an kai hare-hare a gidan yari da sansanin 'yan sandan kwantar da tarzoma da kuma makarantar firamare.

Kakakin rundunar tsaro ta hadin guiwa JTF, Laftanar Kanal Sagir Musa ya tabbatar wa da BBC aukuwar lamarin.

Sai dai yace a yanzu ba zai iya bada cikakken bayani game da girma ko illar da hare-haren suka yi ba.

Haka kuma kawo yanzu babu wani ko wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin.

Mazauna garin na Bama sun ce sun kuma dinga jin harbe-harbe, bayan hare-haren na safiyar ranar Talata.

Yayin da a Banki kuma wasu mazauna garin suka ce sun shige daji saboda tashin hankalin.

Garuruwan biyu dai na kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Kamaru.

Jihar Borno dai ta kwashe shekaru tana fama da tashin hankali, musamman hare-hare da a wasu lokutan a baya, kungiyar nan ta Jama'atu Ahlul sunnah lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram ta sha daukar alhakin kai su.