An kashe mutane 55 a jihar Borno

Maiduguri
Image caption Jihar Borno na fama da hare-haren kungiyar Boko Haram

Akalla mutane 55 ne aka kashe a lokacin da wasu 'yan bindiga suka kaddamar da hare-hare a garin Bama na jihar Borno a arewacin Nigeria, a cewar jami'an tsaro.

Harin wanda rundunar tsaro a jihar ta ce tana zargin 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai a ranar Talata, ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan sanda 22, jami'an tsaron gidan yari 14 da kuma sojoji biyu.

Har ila yau an kashe fararen hula hudu da kuma maharan 13, a cewar mai magana da yawun rundunar tsaro ta hadin gwiwa a jihar ta Borno Kanar Sagir Musa.

Maharan sun kuma kubutar da fursunoni 105 a lokacin harin.

Sannan suka kona ofishin 'yan sanda na Bama, da barikin soji da wasu gine-ginen gwamnati, kamar yadda Sagir Musa ya shaida wa BBC.

Karin bayani