An hallaka mutane 55 a Bama

'Yan Kungiyar da ake kira Boko Haram
Image caption 'Yan Kungiyar da ake kira Boko Haram

Rundunar sojojin Nigeria ta tabbatar da cewa jumlar mutane 55 ne suka rasa rayukansu a sakamakon wani hari da aka kai garin Bama a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nigeria. Ana zargin yan kungiyar da ake yiwa lakabi da Boko Haram ne suka kai harin.

Kakakin rundunar hadin guiwa ta JTF a Jihar Borno, Laftanar Kanar Sagir Musa, ya bayyana cewa an hallaka 'yan sanda 22 da gandirobobi 14 da sojoji 2 da kuma farar hulla 4, yayin da aka hallaka wadanda ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne 13.

Haka nan kuma 'yan bindigar sun fasa wani gidan kaso, inda suka sallami fursunoni 105. Laftanar Kanar Sagir Musa, ya kuma ce an kona wurare da dama a cikin garin na Bama, wadanda suka hada da ofishin 'yan sanda da barikin soji da wasu gine ginen gwamnati.

Rundunar sojojin ta ce wadanda suka kai harin suna sanye ne da kayan sarki irin na sojoji.