Wata cuta na barazana ga rogo

rogo
Image caption rogo

Masana kimiyya na gargadin cewar wata cuta da ta lalata rogo a yankin Gabashin Afrika a yanzu kuma ta fara yaduwa zuwa wasu yankuna na nahiyar, har ta fara isa kasar Angola.

Mutumin da aka hada gwiwa da shi wajen kafa wata kungiyar kula da noman Rogo a duniya, Claude Fauquet ya ce cutar a halin yanzu tana yin barazanar watsuwa zuwa yammacin Afrika, har zuwa cikin Nijeriya, wadda ita ce kasar da ta fi kowace samar da Rogon a duniya.

Daruruwan miliyoyin jama'a ne suke dogaro da rogon a matsayin abinci.

Masana na cewa a halin da ake ciki, ana asarar ton miliyan hamsin na rogo a kowace shekara, kuma idan ba an dauki wani mataki ba, na hana yaduwar cutar, asarar da za a yi a gaba zata iya zama mai matukar muni.