Ministan tsaron Libya ya fasa yin murabus

Libya
Image caption 'Yan bindiga sun girke makamai a ma'aikatun Shari'a da na harkokin waje

Ministan tsaro na kasar Libya ya janye murabus din da yayi, sa'o'i kadan bayan da ya ce zai bar mukamin.

Tun da farko Mohammed al-Barghathi ya yanke shawarar ajiye mukamin na sa sakamakon mamayar da 'yan bindiga suka yi wa ma'aikatun shari'a da na harkokin wajen kasar.

Sai dai daga bisani Fira Ministan Libya Ali Zeidan, ya shaida masa cewa kada ya gabatar da takardar murabus din na sa ga taron Majalisar ministoci.

Masu dauke da makaman da suka mamaye ma'aikatun sun bukaci a amince da dokar da za ta hana dukkan mutanen da suka rike mukami a zamanin marigayon Kanar Gaddafi samun hawa irin mukami.

A ranar Lahadi ne majalisar dokoki ta amince da dokar, mako guda bayan da 'yan bindiga suka fara mamayar.

'Yan bindigar sun ce ba za su bar ma'aikatunba har sai an amince da dokar da za ta hana jami'an Gaddafi rike mukamai a kasar baki daya.

Wakiliyar BBC Rana Jawad a birnin Tripoli, ta ce sabuwar dokar siyasar za ta yi tasiri a kan Mr Barghathi idan ta fara aiki.

Ta kara da cewa da alamu ya yi niyyar murabus din ne domin janye jiki kafin a kore shi.

Karin bayani