An gano Amurkawa ukun da suka bata a Ohio

Biyu daga cikin matan da aka gano, bayan sun bata a shekarun baya a Amurka
Image caption Biyu daga cikin matan da aka gano, bayan sun bata a shekarun baya a Amurka

'Yan sanda a Amurka sun gano wasu mata uku da suka bata shekaru da dama da suka wuce, a wani gida da ake tsare da su dake Cleveland, a jihar Ohio.

Daya daga cikin matan Amanda Berry, da ta bace shekaru goma da suka gabata, lokacin tana da kimanin shekaru goma sha shida ta samu kubuta daga gidan ne tare da taimakon makwabcin gidan da ake tsare da su.

Daya matar kuma mai suna Gina DeJesus, ta yi batan dabo ne lokacin da ta ke kan hanyarta ta komawa gida daga makaranta, a shekara ta 2004, lokacin tana da kimanin shekaru goma sha hudu.

Ta ukunsu kuma Michelle Knight, ta bace ne tun a cikin shekara ta 2002, lokacin da take da shekaru ashirin da haihuwa.

Miss Berry dai ta ce sunan wanda ya sace su Ariel Castro.

Nan da nan dai Amanda Berry ta buga waya sashen masu aikin taimakon gaggawa, jim kadan bayan makwabcinsu ya ceto ta.

Rahotanni dai sun ce an kuma samu wasu kananan yara a gidan da aka tsare matan, kana kuma an cafke wani mutum mai shekaru hamsin da biyar da haihuwa.