MDD na fuskantar barazana

Annobar Kwalara a Haiti
Image caption Annobar Kwalara a Haiti

Mutannan da annobar kwalara ke ci gaba da addaba a kasar Haiti sun debawa Majalisar dinkin duniya watanni biyu na ta fara tattaunawa akan kudadan diyya na biliyoyin dalolin da za'a basu ko kuma ta fuskanci shari'a.

Mutanan da annobar ta shafa, da suka hada da iyalan mutane dubu takwas da kuma wasu daruruwan dubunnai da suka kamu da cutar kwalara na zargin MDD da nuna halin ko in kula inda ta kyale dakarun wanzar da zaman lafiyar ta su gurbata ruwan kasar da cutar kwalara.

Annobar kwalarar ta fara ne a kusa da wani sansanin sojojin Majalisar dinkin duniya inda wasu bututu da bahaya ke bi suka huje suna ke yoyo.

Hakanan kuma ana jibge bahayar a wajan sansanin dake kusa da wani kogi.

Daya daga cikin kwarararun ma'aikatan Majalisar dinkin duniya kan cutar kwalarar ta yarda cewa hakan na iya faruwa.

Karin bayani