Ana ci gaba da zaman dar-dar a Bama

Garin Bama na jihar Borno a Najeriya
Image caption Titunan garin Bama sun yi tsit bayan harin da aka kai ranar Talata

Ana ci gaba da zaman dar-dar a garin Bama dake jihar Borno, arewacin Najeriya, sakamakon hare-haren da wasu 'yan bindiga suka kai.

Harin yayi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 55.

Sai dai Rundunar Hadin gwiwar samar da tsaro JTF a jihar Bornon ta samu nasarar hallaka goma daga cikin 'yan bindigar, tare da cafke mutum guda.

'Yan bindigar dai sun kai farmaki ne cikin gidan yari, da caji ofisoshin 'yansanda da kuma barikin soji, har ma da wasu gine-ginen gwamnati dake garin na Bama suka kone su kumus.

Kakakin Rundunar Hadin gwiwar samar da tsaro a jihar Borno Laftanal Kanal Sagir Musa, ya yi wa BBC karin bayani cewa yan bindigar sun kai hari kan caji ofisoshin 'yansanda da barikin soji da gidan yari dake garin na Bama.

Rundunar ta JTF ta ce dukkannin fursunoni dari da biyar din dake gidan yarin sun arce.

Wani mazaunin garin na Bama ya shaidawa BBC ta wayar tarho a daren jiya cewa suna cikin halin fargaba, yayin da da dama suka tsere daga garin.

Harin baya bayan nan ya kasance mafi muni da aka taba kaiwa a garin na Bama, da yanzu haka aka kara tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen garin.