Matan da aka sace a Amurka sun ci wuya

Matan da aka sace a Amurka

Ana kara samun haske game da yanayin da aka tsare matan nan uku har tsawon kusan shekaru goma a wani gida a birnin Cleveland na Amurka.

Yansanda sunce an gano igiya da sarkoki a gidan, sannan suka ce an kuma ware matan da junansu.

Wata majiya a kusa da masu bincike ta shedawa BBC cewar an yi wa daya daga cikin matan mummunan duka, har ta zubar da cikin da ta dauka.

Wata kuma ta yi juna biyu da yawa, ta kuma zubar da da yawan.

Biyu daga cikin matan, Amanda Berry, da Gina DeJesus sun koma gida inda aka yi masu kyakykyawar maraba.

Mahaifiyar ta ukun - Michelle Knight -- ta ce har yanzu ba ta ga diyarta ba.

Kwamandan yansanda a Cleveland, Thomas McCartney ya bukaci jama'a da su kwantar da hankalinsu:

Karin bayani