Mutane sama 1000 ne suka mutu a Bangladesh

Bangladesh
Image caption Jama'a da dama sun rasa 'yan uwansu a bala'in da ya afku

Sojoji a kasar Bangladesh sun ce adadin mutanen da suka mutu a faduwar ginin masana'anta mafi muni a kasar ya zarta 1000, a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto.

Ko a ranar Juma'a da safe jami'ai sun ce an gano gawarwakin mutane 28.

Rushewar ginin na daya daga cikin bala'i mafi muni da ya auku a fannin masana'antun kasar.

Mahukunta sun ce kimanin 2,500 ne suka samu raunuka a hadarin wanda ya faru ranar 24 ga watan Afrilu - kuma ba a san adadin mutanen da ke cikin gininba.

Ana saran a nan da ranar Lahadi za a kammala aikin ceton. Daga nan ne kuma za a debe kuraguzan ginin.

Kyaftin Shahnewaz Zakaria, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an sake gano gawarwakin mutane 130 a ranar Alhamis.

Yawancin mutanen halittarsu ta fara sauyawa, amma za a iya gane su da wayoyin salular da ke aljihunansu ko kuma katunan shaida, kuma yawancinsu mata ne.

Ginin na dauke da masaku da yawa, kuma tuni jami'ai da dama ciki harda mai gidan - suka gurfana a gaban kuliya ana tuhumarsu da kisan mutane ta hanyar sakaci.

Jama'a sun yi zanga-zanga suna kiran da a yanke wa mai gidan hukuncin kisa, yayin da ma'aikan masakun suka yi zargin cewa an tilasta musu aiki a gidan duk da cewa an san bangwansa ya tsattsage.

A ranar Laraba ne Bangladesh ta sanar da rufe wasu masaku 18 saboda batun tsaron da kuma damuwar da ake ci gaba da nuna wa kan tsaron lafiyar ma'aikata a kasar.

Karin bayani