Hezbollah na dakon makamai daga Syria

afb
Image caption Shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah

Kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Labanon, wato Hezbollah, ta ce Syria za ta samar mata abin da ta ce makamai da za su sauya yadda al'amura suke a yanzu.

Shugaban kungiyar, Hassan Nasrallah, ya ce bada sabbin makaman wani martani ne kan hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama kan abin da akayi amannar makamai ne da Syria ta turawa Hezbollah a asirce.

Har ila yau ya ce kungiyarsa zata marawa Syria baya kan duk wani kokari na fattatakar Isra'ila daga Tuddan Golan.

A shekara ta 2006 ne Isra'ila ta fafata da kungiyar Hezbollah ta kuma ce baza ta bar kungiyar ta habaka makamanta ba.

Hezbollah na baiwa mayakan gwamnatin Syria makamai, a yakin basasar da suke da 'yan tawaye.

Karin bayani