Najeriya: An kai gawar 'yan sanda 88 asibiti

Wasu daga cikin jami'an tsaron da aka yiwa kwanton bauna
Image caption Wasu daga cikin jami'an tsaron da aka yiwa kwanton bauna a Jihar Nasarawa, Najeriya

A Najeriya, wata majiya ta asibiti ta tabbatarwa BBC cewa an kai gawarwakin 'yan sanda tamanin da takwas, wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kwanton baunar da wasu 'yan bindiga suka yiwa jami'an tsaro a Jihar Nasarawa da ke arewacin kasar.

Ranar Laraba rundunar 'yan sandan Jahar ta Nasarawa ta bayyana cewa an kashe akalla 'yan sanda ashirin da uku, yayin da wadansu da dama suka jikkata, kuma an nemi kimanin jami'ai goma sha bakwai an rasa.

Hukumomi a Jihar sun ce 'ya'yan wata haramtaciyyar kungiyar 'yan bindiga da ake kira Ombatse ne suka yi wa jami'an tsaron kwanton bauna lokacin da suke kokarin farautar 'ya'yan kungiyar a ranar Talatar da ta gabata.

Wadansu rahotanni dai sun ce 'yan sandan da aka kashe sun kai dari a kauyen Alakyo dake karamar hukumar Lafiya.