An kashe 'yan sanda 23 a jihar Nasarawa

Jami'an tsaro a Najeriya
Image caption Jami'an tsaro a Najeriya

Rundunar 'yan sandan jahar Nasarrawa ta tabbatar da cewa an kashe akalla 'yan sanda ashirin da uku, yayinda wasu da dama suka jikkata.

Rundunar ta kara da cewa kimanin jami'an 'yan sanda goma sha bakwai ne aka nema aka rasa, bayan wani harin kwantan bauna 'ya'yan wata haramtaciyyar kungiyar 'yan bindiga ta Mbatse dake kauyen Lakyon suka kaiwa jami'an 'yan sandan.

Sun kai musu farmakin ne a lokacin da suke kokarin farautar 'ya'yan kungiyar a ranar talatar da ta gabata.

To sai dai wasu rahotannin na cewa 'yan sandan da aka kashe sun zarta hakan a kauye na Lakyon dake karamar hukumar Lafiya a jahar Nasarawa.