Nassarawa: 'Yan sanda sun nemi a sako mutanensu

'Yan sandan Najeriya
Image caption 'Yan sandan Najeriya

Rundunar 'yan sanda a jihar Nassarawan Najeriya, ta yi kira ga 'yan k’ungiyar Mbatse da su yi wa Allah su sako mata ragowar jami'anta su 17 da ta ce, ke tsare a hanun k’ungiyar a k’auyen Lakiyon da ke K’aramar Hukumar Lafiya a jihar.

Rundunar 'yan sandan ta kuma ce ‘yan sanda talatin ne aka kashe a yayin da tara suka ji raunuka a kwanton ‘baunar da ake zargin 'yan kungiyar sun yi wa 'yan sanda.

Sai dai wasu rahotani sun ce adadin ya fi haka.

Su ma matan ‘yan sandan da aka kashen sun yi zanga-zanga, suna tir da abin da ya auku, suna kuma neman sai a ba su gawawwakin mazajen nasu.

‘Yan k’ungiyar Mbatse suna yin addinin gargajiya ne na k’abilarsu ta Eggon da ke jihar ta Nassarawa.

A can baya dai an sha kabsawa tsakanin ‘yan k’abilar Eggon din da kuma Fulani da ke yankin.

Gwamnati tana tattaunawa a kan tsaro a jihar.