Pakistan: An sace ɗan Yusuf Raza Gilani

Image caption Tsohon praministan Pakistan wanda aka sace ɗansa

A Pakistan wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace ɗan tsohon praministan ƙasar, Yusuf Raza Gilani, yayin wani gangamin siyasa a garin Multan na lardin Punjab.

Wannan dai wani ɓangare ne na irin tashin hankalin da ake cigaba da fuskanta gabanin zaɓen ƙasa baki ɗaya da za'a yi ranar Asabar a Pakistan.

Tsohon praminista, Yusuf Raza Gilani ya faɗawa BBC cewar, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace ɗansa, wanda yake takara yayin da yake yaƙin neman zaɓe.

Yusuf Raza Gilani ya zargi abokan hamayyar siyasa da hannu a sace ɗansa.

Rahotanni dai sun ce, lamarin ya auku ne yayin da wasu 'yan bindiga a mota da kuma kan babura suka soma harbi a wurin kana suka cafke ɗan tsohon praministan, Ali Haider Gilani, kana suka sa shi cikin mota da ƙarfin tsiya.